KALMAR DA ZAKA FADA ALLAH YAYI MAKA GAFARA

Dukkan wanda yake son samun gafarar Allah to ka yawaita ambaton Allah musamman karatun alqurani da kuma abinda ya tabbata na zikiran Annabi ﷺ, wannan itace hanya mafi girma ta samun gafarar Allah bayan inganta tauheedi da Aqeedar bawa.

Ga wadan su kalmomi mu hardace su mu yawaita fadarsu dan samun gafarar Allah,sannan mu koyawa yan uwanmu mu yada su a tsakanin mu.

Zababban masoyina da Manzon Allah ﷺ yana fadawa daya daga cikin Sahabbansw sai yace.

(Shin bazan koya maka ba wadan su kalmomi ba,wanda idan ka fadesu Allah zai gafarta maka?)

idan kazon a gafarta maka sai kace.

لا إله إلا الله العليّ العظيم

LAA ILAHA ILLALLAHUL ALIYIL AZEEM”.

لا إله إلا الله الحكيم الكريم

LAA ILAHA ILLALLAHUL HAKEEMUL KAREEM”

لا إله إلاّ الله سبحان الله ربّ السموات السَّبع وربّ العرش العظيم

LAA ILAHA ILLALLAH SUBHANALLAH RABBIS SAMAWATIS SABA’I WARABBIL ARSHIL AZEEM

الحمد لله ربّ العالمين

ALHAMDULILLAHI RABBIL AALAMEEN

@صحيح الجامع للألباني 2621.

ALLAH NE MAFI SANI.

Allah Yasa Mudace Albarkacin Fiyayyen Halita.

By admin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *