Bayanin Fitar Da Zakka Daga Bakin Sheikh Albani Zariya, Da Kashe Kashenta.
AYAU ZAMUYI BAYANIN ZAKKA KASHI {1} DAGA BAKIN MARGYAYI ALBANI ZARIYA.
Yaku Bayin Allah, Ita wannan dukiya ni’ima ce ga wasu mutane, kuma musiba ce ga wasu. Ni’ima ce ga wanda ya karbe ta da haqqinta, kuma ya kashe ta inda ya kamata, ya bada zakka kuma temaka da ita wannan dukiyar *to wannan dukiyarsa ni’imace gareshi.
Yaku bayin Allah wasu kuma dukiyarsu musifa ce garesu, domin anan duniya basu fitar da haqqin Allah acikin wannan dukiyar ba shine zakka to wannan dukiyarsu musifa ce agaresu, domin tabbas se sunyi nadama a inda yin damanar na rashin cire zakka da basuyi ba baze amfanesu da komai ba.
Ya kai dan’uwana musulmi, ka ba da zakkar dukiyarka kana mai sakin zuciyarka. Ka ba da zakkar dukiyarka, kana mai qudurce wajabcinta a musulunci. Ka ba da zakkar dukiyarka domin biyayya ga Allah da Manzonsa. Ka bada zakkar dukiyarka don dukiyarka ta wanzu a gare ka, albarkarta ta qaru, alherinta ya yawaita, bala’i ya yaye daga gare ka.
Ya dan’uwana Musulmi! Ka dubi ni’imar da Allah ya yi maka na wannan dukiya ba ka same ta ba don qarfin jikinka, ko basirar ra’ayinka. Tsantsar falala ce, kawai ta Allah da karamcinsa, da baiwarsa da kyautatawarsa a gare ka. Dubi wannan dukiya, sannan ka dubi zakkarta, za ka ga zakkar rubu’in ushurinta ne (Rabin rabin daya bisa goma ne) ko a ce, biyu da rabi a cikin dari *(2.5%).* Allah Ya baka da yawa, amma ya gamsu da kadan daga wajenka. Sannan wannan dan kadan din ma amfaninsa kanka zai dawo duniya da lahira.
Yaku bayin Allah, manzon Allah (ﷺ) yace, “Babu wata dukiya da za ta tawaya saboda fita da zakka.”
Allah ya bada ikon fitar da zakka domin Allah.
Dan Allah ‘Yan Uwa Kuyi Share Zuwa Facebook Twitter Instagram Pinterest Telegram Da Sauran Domin Sauran Al’umma Musulmai.