TAMBAYA DA AKAIWA MALAM.

YAUSHE AKE SANAR DA JAMA’A SUNAN JARIRIN DA AKA HAIFA….?

AMSA:-

Sunnah Ta Bayyana lokacin da ake Sawa jariri suna, acikin Hadisai Maban-banta juna daka cikinsu Akwai.

1- Hadisin da Yake Nuna Mustahabbancin Sanyawa jariri Suna A wuni na Bakwai da Haihuwarsa.,

Hadisin Umair Bin Shu’aib daka Babansa daka Kakansa ( Annabi ﷺ yai Umarni A sanyawa jariri Suna a Wuni Na bakwai da Haihuwarsa, da cire Masa Qazantar daya fito da ita, da kuma Yi Masa Yanka.) Turmuzi Ya ruwaito Wannan Hadisin ( 2832 ) yace: Hadisine kyakkyawa, Albani Ya ingantashi acikin Sahihul Turmuzi.

Da Hadisin Sumra bin Jundab, Wanda Abu Dauda ya sake ruwaitoshi ( 3838 ) Albani Ya Ingantashi acikin Sahihu Abu Dauda.

2- Hadisan Da Suke Nuni Akan radawa jariri Suna aranar da aka haifeshi, Daka Anas Bin Malik Allah Yaqara yarda Dashi Manzan Allah ﷺ yace: ( Acikin Daren jiya an Haifa mini Jariri saina rada Masa Sunan Babana Ibrahim ) Muslim Ya ruwaitoshi ( 2315 ).

Jamhur din Malamai Sun Tafi akan Abunda yafi shine radawa jariri Suna aranar Yini na Bakwai da Haihuwarsa, Sukace Hadisin Anas Bin Malik yana Nuna Halascin Sawa jariri suna Ranar da Aka haife shine Kawai, Baya Nuna Mustahabbanci Bane, Halacci Kawai yake Nunawa .

Duba Al-Mugni ( 9/ 356 ) da Al-AzKãar ( 286 ) da Al- Insaaf ( 4/ 111 ).

Imamul Bukhari Yace: Wanda ya kesan Yin yanka yabari Sai wuni Na bakwai ya radawa jaririnsa Suna, Wanda Bazaiyi Yankaba Ya radawa jaririnsa Suna aranar da aka haifeshi.

Idan Mutum Ya radawa Jaririnsa suna ranar da aka haifeshi da kuma Bari sai a wuni na Bakwai Da Haihuwarsa babu Laifi, Al’amarine Tsakanin Halacci da Mustahabbanci, radawa jariri suna a Wuni na Bakwai shine yafi dai-dai, Amma duk Wanda mutum Yayi Dai-dai ne..

Imamun Nawawi Yace: Ya Halatta sanyawa jariri Suna aranar Wuni na Bakwai da haihuwarsa, ya halatta kafin Wuni na Bakwai din, hadisai Sun bayyana Qarara akan Hakan, Kuma Sahihai. Duba Al-Maj -Mu’u ( 8/ 415 ).

Wallahu A’alamu.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.

By admin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *