Jaruma Ummi Gayu, Ta Cika Baki Da Ikirari A Kannywood,

A Yai Shafin Namu Na Folka Naija Muna Dauke Da HirabDa Dan Jarida Ya Gabatar Da Shida Jarumar Kannywood Mai Suna, Ummulkhairi Usman (Ummi Gayu)
DUK da cewa wasu na ganin Kannywood a matsayin masana’antar da a yanzu ba a samun wani abin a zo a gani, musamman ta ɓangaren ayyukan shirya finafinai, amma kullum ƙara ƙyanƙyasar sababbin jarumai ta ke yi, matasa masu jini a jika.

Ummulkhairi Usman, wadda aka fi sani da Ummi Gayu ko kuma Sa’a a cikin shirin ‘Labari Na’, ta na ɗaya daga cikin matasan jarumai da tauraruwar su ke haskawa a wannan lokaci. Yarinya ce kyakkyawa, son kowa ƙin wanda ya rasa. Ga ta da tsafta, ga fara’a, sannan kuma ga ta da faran-faran da mutane.

Jarumar, wadda haifaffiyar Kaduna ce, ta feɗe wa mujallar Fim biri har wutsiya a game da yadda ta samu damar shiga shirin ‘Labari Na’, ƙalubalen da ta fuskanta a gida kafin a bar ta ta fara fim, nasarorin ta, da dai sauran abubuwa a game da ita a hirar da wakilin mu ya yi da ita kwanan nan.

FIM: Ki faɗa wa masu karatu tarihin ki a taƙaice.

UMMI GAYU: Suna na Ummulkhairi Usman, wadda aka fi sani da Ummi Gayu, sannan kuma Sa’a a cikin fim ɗin ‘Labari Na’.

An haife ni a Kaduna. Na yi firamare da sakandare na duk a Kaduna, a yanzu haka ina ci gaba da karatu na da kuma sauran abubuwan da na sa a gaba.

FIM: Ya aka yi ki ka tsinci kan ki a Kannywood har ki ka samu damar shiga cikin shiri mai dogon zango na ‘Labari Na’?

UMMI GAYU: Alhamdu lillahi. Da farko zan yi wa Allah godiya, ni ma na tsinci kai na ne a cikin ‘Labari Na’, don ban taɓa tunani ba. An ce min Ummi ki zo kin samu wannan fim ɗin, sai na je aka haɗa ni da su Malam Aminu Saira da Naziru Sarkin Waƙa, kuma sun karɓe ni hannu biyu, babu abin da zan ce sai godiya.

FIM: A wane fim ki ka fara fitowa?

UMMI GAYU: Ban taɓa yin fim ba sai fim ɗin ‘Labari Na’.

FIM: Ya ki ka ji a lokacin da aka ɗora maki kyamara?

UMMI GAYU (dariya): Da aka ɗora min kyamara, ina juyawa sai na ga mutane, sai na ji gaba na ya faɗi, ga kuma Malam ina kallon shi. Sai aka ce wa Malam ya yi haƙuri yarinyar nan ta na jin nauyin ka. Haka dai ya fita ya ba mu wuri. Amma duk da haka da na juya sai in ga da mutane, wasu kuma na jira su ga ka yi kuskure, wasu kuma na jira su ga ka yi daidai, da haka cikin ikon Allah abin ya tafi lafiya.

FIM: Ya ki ka ƙare da gida kafin a bar ki ki fara harkar fim?

UMMI GAYU: Wai! Gaskiya an sha fama. Domin lokacin da aka taɓa kira na za mu yi wani aiki, kuma a lokacin mama na ba ta so, haka ma baba na ba ya so, wani lokaci kawai sai na ce bari na fara yi a ɓoye. Na zo ina ɗaukar kaya zan fita, ashe mama na ta na kallo na, sai na ga ran ta bai so ba. Sai kawai na ce mata, “Umma zan je wurin fim ne.” Sai ta ce min a’a ita ba ta so. Sai na ce mata na haƙura, ba zan je ba.

To, a haka dai ina ta fama. Baban mu ya lura ya ga ina son abin, shi kuma sai ya ce da in yi a ɓoye, gara dai in samu manyan da za su tsaya min. Da baba na ya ga manyan daraktoci sun zo sun same shi sun yi masa magana, daga nan sai su ka yarda na fara yi da in je ina yi a ɓoye.

FIM: A ina ki ka samo sunan ‘Gayu’ da ake kiran ki da Ummi Gayu?

UMMI GAYU (dariya): Ummi Gayu? To, ni ma dai na taso ne na ji ana ce wa gidan mu Gidan Gayu; ko yanzu ka shigo Unguwar Sarki ka yi tambaya ina ne Gidan Gayu, za a kawo ka gidan mu ne. Ni na taso ne na ji ana faɗi, sai ƙawaye na su ke kira na da Ummi Gayu, shi ne sai sunan ya bi ni.

FIM: Bayan ‘Labari Na’, akwai wasu finafinan da ki ka yi?

UMMI GAYU: Kamar yadda na faɗa maka, ‘Labari Na’ ne kawai na yi zuwa yanzu. Amma kuma ka san shi fim ne ɗaya tamkar dubu.

Ummi Gayu… Son kowa ƙin wanda ya rasa
FIM: In ki ka ce shi fim ne ɗaya tamkar dubu, kenan duk sauran finafinai ba su kai ba, sai wanda ke ki ke ciki?

UMMI GAYU: Gaskiya ‘Labari Na’ duniya ne! Duniya ta san da shi, don haka ‘Labari Na’ ɗaya ne tamkar dubu.

FIM: Wane irin ƙalubale ki ka fuskanta a masana’antar bayan shigowar ki?

UMMI GAYU: To, ba za a rasa ba. Wasu ƙiri-ƙiri za ka ga sun nuna maka ba su son ka, wasu kuma za su nuna maka su na son ka. Ni alhamdu lillah, ba na faɗa da kowa, ko da mutum ya yi min kallon banza, ni ba ta tashi na ke ba, ni abin da ya kawo ni shi na ke yi.

FIM: Ana cewa ana yi wa mata kan-ta-waye a masana’antar shirya finafinai na Kannywood in su ka shigo. Ya abin ya ke? An taɓa yi maki?

UMMI GAYU: Wallahi ni ma ina jin sunan ne, wai kan-ta-waye. Ban kuma taɓa cin karo da wani abu makamancin haka ba.

FIM: Kafin ki fara fitowa a shirin ‘Labari Na’, babu wani ɗan fim da ya ke fakewa da harkar ya ke zuwa wurin ki da maganar soyayya?

UMMI GAYU: Ban taɓa soyayya da ɗan fim ba.

FIM: Waɗanne nasarori ki ka samu a harkar fim?

UMMI GAYU: Na samu nasarori da dama, mutane na kira na, ana kawo min kyaututtuka, na karɓi awad, duk inda na shiga za ka ji ana Ummi ‘Labari Na’, wasu ma “‘yar hassada” su ke ce min!

FIM: To a zahiri ki na da hassadar?

UMMI GAYU (dariya): Wayyo Allah! In ma za ka tambaye ni menene hassada, ni ban ma san shi ba.

FIM: Wacece madubin ki a Kannywood?

UMMI GAYU (Dariya): Ni dukkan su madubi na ne.

FIM: Ko akwai jarumin da ya taɓa kawo maki goron gayyata na ku fara soyayya?

UMMI: E, akwai waɗanda su ke kawowa, amma na ƙi amsa.

FIM: Menene dalilin ki na ƙin amsa?

UMMI GAYU: Aiki na zo ba soyayya ba. Mu na mu’amala na kasuwanci, ba wai soyayya ba.

FIM: Kenan ba za ki iya auren ɗan fim ba?

UMMI GAYU: Aure ka ce, aure nufi ne na Ubangiji. In Allah ya ƙaddara min za a iya wannan. Amma dai a’a.

FIM: Ummi Gayu ta taɓa aure?

UMMI GAYU: Ummi Gayu ta taɓa aure, na kuma haihu.

FIM: Ganin cewa a yanzu tauraruwar ki ke haskawa, idan ki ka samu miji za ki yi aure ko sai kin cimma burin ki a harkar fim?

UMMI GAYU: Ko yanzu in na samu miji zan yi aure na.

FIM: Da fim kaɗai ki ka dogara ko kuma ki na haɗawa da wata sana’ar?

UMMI GAYU: E, ina wata sana’ar ban da fim.

FIM: Menene burin ki game da wannan harka ta fim?

UMMI GAYU: Buri na in zama jarumar da jama’a za su yi alfahari da ni, ni kuma in riƙa taimakon jama’a, buri na kenan.

FIM: Ki na da burin ki riƙa shirya fim na kan ki kamar yadda wasu jaruman su ke yi?

UMMI GAYU: Ina da wannan burin. Ni ma in ga gani nan ina shirya nawa fim ɗin, ina ɗauko jarumai ina sakawa a fim, ina biyan su kuɗi, ina cewa ga yadda za a yi.

FIM: Waɗanne ƙasashe ki ka taɓa zuwa?

UMMI GAYU: Na je Saudiyya aikin Umra. Amma akwai ƙasashen da na ke da burin zuwa, kamar Amerika da Landan.

FIM: Kasancewar yawancin ‘yan matan da ke shigowa Kannywood a yanzu jaruman waƙa ne, ya Ummi ta ɗauki kan ta – jarumar waƙa ce ko ta fim?

UMMI GAYU: Ni jarumar duka ce. Ina yin fim, ina kuma bidiyon waƙa. Amma na fi ba da ƙarfi a ɓangaren fim ba waƙa ba.

FIM: Wane kira ki ke da shi ga abokan sana’ar ki, musamman mata?

UMMI GAYU: Ni mace ce, don haka ina kira ga dukkan mu da mu riƙe mutuncin kan mu, saboda wata rana za mu zama iyaye. Allah dai ya sa mu dace.

“Gaskiya ‘Labari Na’ duniya ne!” inji Ummi Gayu.

FIM: Shin Ummi Gayu tarbiyya ta zo koyarwa ko neman kuɗi?

UMMI GAYU: Ni tarbiyya na zo koyarwa, saboda ana nuna wa mutane wasu abubuwan da su ke yi a rayuwar da cewa ba shi da kyau. Ka ga kamar ai a ‘Labari Na’, rol ɗin da aka ba ni na ‘yar hassada, ai akwai mutane irin haka, to mu na faɗakarwa ne da kuma nuna halayyar wasu mutane, a ƙarshe kuma sai a nuna yadda su ke nadama da sauran su.

FIM: Menene saƙon ki ga masoyan ki?

UMMI GAYU: Masoya na ina yi masu fatan alkhairi, don Allah su ci gaba da yi mana addu’a.

FIM: Mun gode, Ummi Gayu.

UMMI GAYU: Ni ma na gode.

Domin Samun Sabbin Labarai Kannywood A Kan Koci Sai Ku Dannah Muna Comment Da Kuma Kasancewa Da Mu A Wannan Zauren Na Folknaija.com.ng A Kowanne. Lok Lokaci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *