Yadda Auren Tijjani Asase ya zama mai igiya biyu Masana’antar Kannywood,

JARUMIN nan na Kannywood wanda ya ƙware wajen fitowa a fim a matsayin ɗan daba, Tijjani Abdullahi (Asase), yanzu ya shiga sahun ‘yan fim masu mata biyu.

A yau Asabar, 4 ga Maris, 2023 aka ɗaura auren sa da sahibar sa, Khadija Ɗahiru Mu’azu Kyalli, da misalin ƙarfe 11 na safe a Masallacin Baballe Ila da ke unguwar Gyaɗi-Gyaɗi, Kano.

Ɗaurin auren ya samu halartar jama’a da dama.

Amarya Khadija da ango Asase tare da abokan arziki.

An shafe tsawon kwana uku ana gudanar da shagulgulan biki inda aka fara da majalisin yabon Annabi da kuma saukar karatun Alƙur’ani a ranar Laraba. A shekaranjiya Alhamis aka yi Bikin Larabawa a wajen shaƙatawa na Banana da ke bayan Kantin Jifatu a Titin Zariya, sai kuma jiya aka shirya gagarumar dina a Ali Jita Events Centre.

Taron bikin ya samu halartar jama’a da dama waɗanda su ka je don taya ango da amarya murna.

Wannan aure dai shi ne na uku da Asase ya yi. Na farkon, Allah ya yi wa matar rasuwa, daga baya ya auri wata, sai kuma yanzu da ya ƙara ɗaya.

Asase furodusa ne wanda ya shirya fim mai dogon zango mai suna ‘A Duniya’ inda ya ke fitowa a matsayin Sanda, ogan ‘yan daba.

Allah ya ba da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin sa da Khadija da sauran iyalin sa, amin.

Mata adon gari a wajen walimar auren Tijjani Asase da Khadija Ɗahiru Mu’azu Kyalli.

Tijjani Asase na yi wa mahalartan walimar auren sa da Khadija fatan alheri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *