Yadda Wani Tsoho Yashiga Zumudi – Bayan Ya Auri Jikanta Tai,
A Darasin mu na baya mun kawo wasu dalilai da ke sa ‘yan mata soyayya da tsofaffin maza. Yanzu kuma mun binciko wasu dalilai da ke sa mata masu ƙarancin shekaru auren mazan da su ka yi jika da su.
Binciken kimiyya ya tabbatar da ƙwaƙwalwar ‘ya mace ta fi ta ɗa namiji buɗewa da saurin balaga. Wannan ya na ɗaya daga cikin dalilan da su ka sa mata su ke kin mu’amala da sa’annin su. Ga wasu dalilai da ke sa wasu ‘yan matan auren dattijai.
1: Dattaku: Mata su na son mutum mai kamanta gaskiya. Mai magana guda. Wannan ya na daga cikin dalilin da su ka sa ‘yan mata su ke sha’awar auren dattijon namiji.
2: Gudun Yaudara: Shi dattijon mutum ba a san shi da yaudara ba. Ganin akasarin dattawa su ma su na da ‘ya’ya mata har ma da jikoki ya sa da wuyar gaske ya yi alƙawarin auren mace ya fasa. Mata kuwa, musamman wacce aka taɓa yaudarar ta ko aka yaudari wata ta kusa da ita, gudun yaudarar maza masu ƙarancin shekaru ya kan sa mata su gwammace auren dattijo mai cika alƙawari.
3: Iya Lallaɓa: Shi dattijon namiji ya san dabaru da hanyoyin da zai bi domin ya lallaɓi mace a lokacin da ya ɓata mata rai ko aka ɓata mata rai ko kuwa ran ta ya ɓaci, saɓanin shi namiji mai ƙarancin shekaru. Hakan ya sa mata su ke son auren dattijo.
4: Haƙurin Zama Da Mace: Ya na daga dalilan da ke janyo hankalin mata masu ƙarancin shekaru auren dattijai. Su dattawa su na da gogewa wajen yadda za su zauna da mace saboda jimawa da aure da kuma yawan mu’amala da mutane.
Shi dattijo ba kamar namiji mai ƙarancin shekaru ba ne wajen juriya da haƙurin zama da mace. Wannan ya sa ƙananan mata su ka fi sha’awar su auri dattijo auren su ya ɗore maimakon auren yaro da zai iya kasa haƙurin zaman aure da su.
5: Abin Duniya: Akasarin dattawan da ke sha’awar auren mata masu ƙarancin shekaru masu riƙe da muƙamai ne ko masu sarauta ko manyan ‘yan kasuwa ko kuma manyan ‘yan siyasa da su ke da abin duniya a jibge.
‘Yan mata sun gwammace su auri irin waɗannan tsofaffin su shiga daula maimakon auren saurayi su yi zaman talauci.
6: Kariya: Akwai matan da ke auren dattawa waɗanda su ke ma yin hidimar auren da kan su. Ko kuma iyayen su su aura musu su. Irin wannan auren wani lokaci ana yin sa ne saboda samun mafaka daga wani abin ƙi da yarinyar ta yi a lokacin da ta ke budurwa. Akwai yaran mata da su ka yi gagarar da su ke rasa mazan aure, hakan ya sa ko dai su da kan su su aura wa kan su dattawan saboda kare yawa ko kuma iyayen su su laƙaba wa wasu aminan su ko ‘yan aikin su su aura domin a wuce wajen.
Mu fatan mu ko ma da yaya aka yi auren, Allah ya ba da zaman lafiya da lafiyar da ma’aurata za su iya gamsar da juna da samun zuriya mai albarka.A
Allah Yasa Mudace.