Fitacciyar jaruma Ummi Saleh Ahmad (Ummi Rahab) ta yi nisa wajen juya akalar angon ta, wato fitaccen mawaƙin nan kuma jarumi, Shu’aibu Ahmad Abbas (Lilin Baba), musamman wajen mu’amalar sa da soshiyal midiya.

A da, ba a san Lilin Baba da bayyana duk wani abu da ya danganci iyalin sa ba. In ba domin mujallar ta faɗa ba a ranar ɗaurun sa da Ummi, to da ba kowa ba ne ya san ya na da mata har da ɗa mai zuwa makaranta.

Lilin Baba mutum ne mai yin tsantseni game da iyalin sa, ba ya yarda duniya ta gan su kamar yadda jarumai maza da dama ke tutiya da nuna iyalin su a duniya.

Ali Nuhu, Sani Danja, Adam A. Zango, Sadiq Sani Sadiq, Yakubu Muhammad, Hassan Giggs, Nura M. Inuwa, Abdul Kafinol, Al-Amin Ciroma da Idris Shu’aibu Lilisco na daga cikin ‘yan fim da aka san matan su da ‘ya’yan su a kafafen sada zumuntan.

Ummi Rahab da Lilin Baba a mota
To, shi ma Lilin Baba ya shiga sahu tun daga lokacin da ya auri Ummi Rahab.

Shi da ita yanzu sun mamaye soshiyal midiya da hotuna da bidiyoyin su, inda ake ganin su su na sharɓar soyayya.

Ummi na ta wallafa bidiyoyin ta da angon ta su na sharɓar soyayya

Hakan ya ba masoyan su da mabiyan su mamaki, musamman da yake ba a san nawaƙin da irin wannan halayyar ba.

Ko a lokacin auren su, ko hoton su ba a gani ba a matsayin ma’aurata, domin ba a yi dina a lokacin bikin ba, ballantana a gan su taren.

Wata majiya ta ce Ummi ta so ta halarci walimar da Lilin ya shirya a Kano, amma shi ya hana ta, kuma “hakan bai yi mata daɗi ba.”

Tun kafin auren ma babu wanda ya ga wani hoto da su ke tare kamar yadda aka saba yin hotunan kafin aure (pre-wedding pictures) da ake yayin ɗauka ana bazawa a soshiyal midiya, duk da yake su fitattu ne a cikin al’umma, kuma yawancin ‘yan fim na yin haka.

Kwatsam, a ranar idin Babbar Sallah sai ga ango Lilin Baba ya ɗora hotunan su har kala 10 a Instagram, tare da yi wa mabiyan sa gaisuwar Sallah kamar haka: “Eid Mubarak from this side, Allah ya maimaita mana, me & my wife #shurab2022 @shurab2022 #rabinraina.”

Ita kuma Ummi sai ta bi sahun sahibin nata ta maimaita ɗora hotunan a nata shafin.

Masoyan su da abokan sana’ar su sun yi murna matuƙa da ganin hotunan, inda su ma su ka taya su rarrabawa a shafukan su tare da yi masu fatan alheri.

Haka kuma a ranar Talata, 26 ga Yuli, 2022 Ummi Rahab ta ɗora sababbin hotuna waɗanda su ma sun kai kala 10 a shafin ta, sannan ta yi rubutu da Turanci a ƙasan hotunan, ta ce, “Reason behind my happiness. As you take good care of us, u make me happy.

“May Almighty Allah guide u and protect you everywhere u are. I love you with all my heart. Am so lucky having u as a husband.”

Ma’ana, “Kai ne dalilin farin ciki na, yadda ka ke nuna kyakkyawar kulawa gare mu, ka na sa ni farin ciki.

“Allah (s.w.t.) ya tsare ka, ya kare ka a duk inda ka ke. Ina son ka da dukkan zuciya ta. Na yi sa’a da na same ka a matsayin miji.”

Auren masoyan biyu sai dai a ce tubarkallah, domin kuwa waɗannan hotunan sun nuna lallai su na cikin farin ciki da jin daɗin amarci. Kuma da ma Lilin Baba kowa ya shaida shi jarumi ne wurin kula da iyalin sa.

Duk wanda ya ga Ummi ya san cewa lallai yanzu hankalin ta ya ƙara kwanciya, domin ta auri wanda ta ke ƙauna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *