Abinda Ya Raba Adam A Zango Da Ummi Rahab Jarumar Kannywood,

Shekaranjiya, labarin rincaɓewar taƙaddamar da ke ruruwa tsakanin Adam A. Zango da Ummi Rahab ya bazu bayan gargaɗin da jarumar ta wallafa a Instagram inda jarumar ta faɗa wa tsohon ubangidan nata cewa ya daina abin da ta kira da ɓata mata suna da ya ke yi ko kuma ta tona masa asiri.

Ya zuwa yanzu dai fitaccen jarumin kuma mawaƙi bai ce uffan game da wannan al’amarin ba, illa iyaka dai wasu shafukan soshiyal midiya sun wallafa guntun bidiyon wata hirar kai-tsaye da aka yi da shi a soshiyal midiya inda ya ce ya sallami Rahab ne bayan da ta ƙi bin umurnin sa na ta riƙa gudanar da rayuwar ta bisa turbar da ya ɗora ta a kai.

Wata majiya ta kusa da jarumin ta shaida wa mujallar Fim cewa duk wani makusancin jarumin da ya tura saƙo a kan jan-kunnen da Rahab ta yi a Instagram ɗin, Zango da kan shi ya ke kiran sa ya ce masa ya goge. Magoya bayan sa sun ce hakan da ya yi ya nuna dattaku, kuma ya tabbatar wa da duniya cewa shi ba tsaran yin ta ba ne.

Adam A. Zango da Ummi Rahab lokacin da duniya na kwance lafiya
Shin me ya jawo husumar ne tun da fari?

Adam A. Zango dai ya nuna wa Ummi Rahab ƙauna tun ta na ƙarama. Ya shirya fim ɗin ‘Ummi’ da ita da nufin mayar da ita fitacciyar jaruma yarinya. An yi wata waƙa a cikin fim ɗin mai taken ‘Kin Zamo Takwara Ummi’, inda Jamila Nagudu ta fito a matsayin mahaifiyar Rahab da Haidar, babban ɗan Zango.

Daga baya, sai aka daina jin ɗuriyar Rahab a Kannywood gaba ɗaya har kusan tsawon shekara shida. Ana nan, kwatsam, sai kuma aka ga ta sake ɓullowa a masana’antar. Ya zuwa lokacin dawowar tata, ta ƙara girma, ta zama wata ‘yar kyakkyawar budurwa, son kowa ƙin wanda ya rasa. Nan da nan ta kasance tauraruwa mai haske a kamfanin Adam A. Zango na ‘White House Family’. Zango ya ɗauke ta tamkar ‘yar cikin sa, domin kuwa ko a kamfanin nasu da ‘Yar Autar Zango ake kiran ta. Sai da ta kai mutane da dama su na tsammanin cewa ɗiyar Zango ce ta cikin sa saboda irin abubuwan da ya ke yi mata. A yadda wasu su ka faɗa wa mujallar Fim, fim mai dogon zango na ‘Farin Wata Sha Kallo’ ma da Adamun ya ƙirƙira, don ita ya yi shi.

Amma kuma ba zato ba tsammani sai aka ji sun rabu, dutse a hannun riga. Zango ya maye gurbin ta da wata jarumar a fim ɗin nasa.

Ita kuma kamar an kwanto ɗaurarre. Sai ta shiga tallata kan ta a soshiyal midiya ba ji ba gani. A kusan kullum sai ta ɗauki hotuna da bidiyoyi ta tura a Instagram da Tiktok, waɗanda waɗansu kuma ke kwafa su na ƙara turawa. Wasu daga cikin bidiyoyin nata su na ƙunshe da habaici da shaguɓe. Da yake kyakkyawa ce, kuma ta kan yi hotuna a cikin yanayi na tsiwa da gwanancewa wajen aktin da kuma kwalliya, sannan ga ta da fara’a, kafin ka ce kwabo sai da ta kai babu ‘yar fim a Kannywood da fuskar ta ta ke yawo a soshiyal midiya kamar Rahab.

Labarin cewa sun rabu da Zango kuma ya yaɗu, musamman da aka ga ta koma ɓangaren su mawaƙi Lilin Baba da su Sir Zeesu, waɗanda su ka fito da sabon fim mai dogon zango mai suna ‘Wuff!’, tare da Ummi Rahab a matsayin jarumar shirin.

Tun bayan dawowar ta, wakilan mujallar Fim sun yi ƙoƙari su zanta da ita a game da barin ta industiri da dawowar ta, amma hakan bai samu ba. Sai kuma ga shi wannan taƙaddamar ta ɓarke.

Wata majiya ta shaida wa wakilin mu cewa ana zargin wani matashi mai suna Yaseer M. Ahmad, wanda su ke hulɗa da Rahab na tsawon shekaru da dama, wai shi ne ya sanya ta ta yi wannan rubutun na jan-kunnen Zango a Instagram. Kuma ana ganin dukkan abubuwan da yarinyar ta ke yi sanya ta ake yi don kawai ta baƙanta wa Zango rai.

Ganin yadda mutane ke ta tambayar su waye iyayen yarinyar da kuma inda ta fito, da batun ɓatawar su da Zango, wakilan mu sun ƙara ƙoƙarin zantawa da jarumar da shi kan sa tsohon ubangidan nata, amma haƙar su ba ta cimma ruwa ba.

Don haka wakilin mu ya samu ɗaya daga cikin makusantan Zango na ƙut da ƙut don samun amsoshin tambayoyin da mutane ke yi.

Aminin Zango ɗin, wanda ba zai so mu bayyana sunan sa ba, ya amsa tambayar da wakilin mu ya yi masa kan inda Adam A. Zango ya samo Ummi Rahab, ya ce gaskiya shi bai san waye ya kawo ta wajen jarumin ba, bai kuma san waye sila ba, kuma bai san sa’ilin da su ka haɗu ba.

Sai dai game da irin tarbiyyar da ake cewa Zango ya yi mata, sai ya ce, “Ya yi mata tarbiyya kamar yadda zai yi wa ‘yar sa tarbiyya. Yadda ya ɗauke ta, har waɗansu na zargin cewa ‘yar sa ce, domin har gidan sa ya ɗauke ta ya dawo da ita. Daga baya kuma ta koma gida, ta daina fim kusan shekara goma.

“To, abin ya na ran ta na yin fim ɗin. Sai a gida aka damu dai ta na sha’awar yin fim ɗin. Waɗanda su ke riƙon ta sai su ga cewa tunda shi da ma can ya taɓa riƙe ta kamar ‘ya, kuma ita ga abin da ta ke so, kawai ta dawo harkar fim.

“Ta dawo harkar fim. Ya karɓe ta, ya ce zai shige mata gaba. Ka ga ‘still’ dai ta na zama kamar ‘yar sa kenan, ko? Saboda in ya ce a’a kada ta yi harkar nan, ta riga da ta yi wayo bai san ta ina za ta faɗa ba ko kuma ta je wani waje. A haka ya riƙe ta.
“Wasu su na zangin akwai soyayya a tsakanin su, wasu kuma su na ganin soyayyar uba da ‘ya ne, to ka ga duk wannan babu tabbas, tunda shi bai fito ya ce soyayyar budurwa da saurayi ba ne. Amma dai ya nuna wa duniya ‘yar sa ce, tunda ita ma ta na ce masa ‘Daddy’. In da wata soyayyar ma, bai fito ya nuna wa duniya ba.

“To, daga baya kuma a ‘live video’ ɗin da ya yi, ya ce shi ya so ya yi mata tarbiyya ne, duk abin da za ta yi wanda bai da kyau ya hana ta ta hanu kamar yadda zai hana ‘yar sa. Idan kuma ta ce masa a’a, ita ba za ta ji ba, zai iya haƙura da ita, saboda kada wani abu ya zo ya faru daga baya shi za a yi ‘blaming’, tunda kowa ya san shi da ita. A kan wannan mataki ake a yanzu.”

Shin wannan dalilin ne ya sa ya cire ta a fim? Sai mai ba mu labarin ya ce, “Ba wannan dalilin ba ne ya sa ya cire ta a fim ɗin sa. Idan ka kula, an daɗe ma ba a ci gaba da fim ɗin ba saboda ana tunanin za ta dawo a zauna a ci gaba.

“To akwai wani abu guda ɗaya. Idan ka na tare da wanda zai ba ka shawara, yanzu kamar ɗan ka in ka nuna ka yi fushi da shi ko ƙanen ka, idan har ya na yi maka biyayya ya kamata ya dawo ya ba ka haƙuri a sasanta, ba kuma a ci gaba da rashin jituwar ba. To ba ci, ba cinyewa, kuma mutane sun ƙosa su yi wani abu. To ka ji yadda aka yi. Tunda ba ta da halin dawowa ta bada haƙuri a yi rayuwa tare, shi ya sa ya ga gara ya ci gaba da fim ɗin shi.

“Kuma ya ce ko yanzu idan rol ya kira ta ta dawo zai dawo da ita cikin ‘Farin Wata’. Ya faɗi wannan a ‘live video’ ɗin da ya yi, har ya tada wannan ce-ce-ku-cen maganar.”

Shin ko a wannan dawowar da ta yi industiri, ta zauna a gidan shi? Majiyar ta ce, “E, ta zauna a gidan shi. Amma da yake ta girma yanzu, kuma ga iyalin shi a gidan, in ta zo Kaduna za a yi aiki za ta zauna a gidan shi, idan an gama sai ta koma Kano.”

Wato kenan iyayen ta ‘yan Kano ne?

“E to, gaskiya wannan ne ni ba ni da masaniya. Ni dai shi na sani kawai. Kuma dai ka ga ni tare na ke da shi. Wannan shi ne.”

Yanzu hannun wa ta ke kenan? Sai ya ce, “Yanzu ta na hannun wani da ta ke iƙirarin yayan ta ne. Sunan sa Yaseer. Shi ne dai yanzu ya ke ‘controlling’ ɗin ta.”

To shi Yaseer ɗin yayan ta ne na jini? Mai ba mu labarin ya ce: “Wallahi duk wannan ba zan iya sani ba. Amma dai a ‘yayan ta’ ni na sani, a yadda ta ke kiran shi.”

Mujallar Fim ta tambayi aminin Zango ɗin abin da zai ce dangane da zargin cewa ‘yan ɓangaren su Lilin Baba ne su ke zuga Rahab ta na yin abubuwan da ta ke yi. Sai ya ce, “E to, ana iya cewa haka. Amma idan ka duba, aiki su ke yi da ita. Duk da ana zargin su na soyayya da Lilin, mutane za su iya cewa a ɓangaren su ta ke.”

Haka kuma ana cewa wannan saƙon gargaɗin da ta wallafa, wasu na cewa Sir Zeesu ne ya saka ta ta yi. Mecece gaskiyar?

A sama: Yasir M. Ahmad da Ummi Rahab a cikin 2016. A ƙasa kuma su ne a bana
Ya amsa: “Ka san magana iri-iri za ka iya ji, kowa zai faɗi albarkacin bakin sa. Amma a iya tunanin mutane, musamman na ɓangaren Adamu, ita ba za ta iya wannan tunanin da za ta faɗi haka ba, saka ta aka yi. Kowa zai iya yin irin nashi tunanin, amma babu wanda ya ke da tabbaci. Babu wanda zai iya faɗa maka ga gaskiyar lamarin.

“Kuma ita akwai ‘voice note’ da ta yi, ta ke cewa duk wanda ya shiga tsakanin ta da Adamu wata rana za su shirya, kuma zai ji kunya. Tunda haka ne, kowa ya zauna a kan wannan matsayin, in akwai ƙauna wata rana za a shirya. Shi ya sa duk wanda ya shiga lamarin, a ƙarshe zai ji kunya.”

Mujallar Fim ta tambaye shi: “A yadda ku ke makusantan sa, wace irin shawara ku ke ba shi game da lamarin nan?”

Sai ya amsa da cewa, “Na rantse da wanda ya halicce ni, idan ya ga wani zai yi magana a kan wannan abin hana shi ya ke yi. Wallahi daga ranar da abin ya fara faruwa faɗa ya ke yi ga duk wanda ya yi ‘posting’ na martani. Shi ya sa ka ga duk wanda ya yi ‘posting’ daga baya za ka ga ya cire.

“Ta ɓangaren shawarar da mu ke ba shi, ka ga ma ya saurare ta? Duk wanda zai kira shi a waya ko ya ke tare da shi abin da ya ke faɗa masa kenan, sai ya ce me zai sa ya saurare ta tunda ba abokiyar yin sa ba ce? Saboda a matsayin ‘ya ya ɗauke ta.

Yarinya da baban ta a da: Ummi Rahab da Adam A. Zango
“To, duk kuma yaron da ya ke tare da mu, in ya yi magana aka ce ya goge, sai ya ce su su na amfani da ita ne don su baƙanta masa, su ma shi ya sa su ke magana.

“Don haka waɗannan abubuwan da na faɗa maka su ne kawai na sani a game da tarayyar su.”

Mujallar Fim ta yi ƙoƙarin jin ta bakin waɗanda ake zargin su ne ka ɗaure wa Rahab gindi ta na yi wa ta Zango tsiwa, wato su Yaseer M. Ahmad, Lilin Baba da Sir Zeesu, to amma su ma shiru. Haka ita ma jarumar, wakilin mu ya kira ta a waya fiye da sau uku tare da aika mata da saƙo, amma har zuwa yanzu ba ta amsa ba.

Ummi tare da ‘ya’yan Adam A. Zango
A yanzu dai kowa ya ja daga, ya na ci gaba da harkokin sa. To amma babu shakka maganar ba ta wuce ba. Ana jin nan gaba kaɗan, idan har ba a kai zuciya nesa ba, sai ɓangarorin biyu sun kafsa. Kuma wannan karon battar ba zai yi wa kowa daɗi ba. Sai dai Allah ya kyauta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *