
Babban furodusa a Kannywood, Alhaji Abubakar Bashir Maishadda, ya bayyana cewa daga harkar fim ne ya samo kuɗin da ya buɗe katafaren shagon nan na sayar da tufafi da ya ƙaddamar a ranar Juma’a, don haka ba harka ce da zai yi wasa da ita ba.
Ya faɗa wa mujallar Fim cewa: “Harkar fim ita ce ni, ka ga kuwa in babu ita babu ni. Ko kuɗin da na buɗe shago, ai da fim na same su. Fim ba sana’ar da zan bari ba ne.”
An yi bikin buɗe shagon mai suna ‘Mai Shadda Textile’ a ranar Juma’a, 30 ga Satumba, 2022, wato shago mai lamba 5 da ke MYCA 7, Plaza, a Titin Gidan Zu, a Kano.
A yayin da ya ke tattaunawa da wakilin mu, Maishadda ya bayyana matuƙar farin ciki, ya ce: “Alhamdu lillah. Babu abin da zan ce wa Allah (s.w.t.) sai dai in gode masa. Na kuma yi farin ciki sosai da Allah ya nuna mani wannan lokaci.
“Kasancewar da ma irin wannan sana’ar mu na yin ta a ɓoye, wannan karon sai mu ka ga ya kamata mu bayyana shi saboda mutane su sani, saboda duk wani abu da ake nema na ɓangaren yaduddika, shaddodi, jakunkuna, takalma, duk mu na da su.
“Kuma in-sha Allahu za mu riƙa ba da farashi irin yadda ake ba da wa a kasuwa. Zai zamana da ka shiga cikin kasuwa ka haɗu da gosulo ran ka ya ɓaci, gwanda ka zo wurin mu ka saya.”
Dangane da yadda zai iya haɗa wannan kasuwancin da sana’ar fim kuwa, furodusan ya ce ai yayar sa da ƙanwar sa ne zai bar wa aikin gudanar da shagon yayin da shi kuma zai ci gaba da harkar sa ta fim.
Ya ce: “Ai wancan kasuwancin ba ni ne a kai ba, yaya ta ce da ƙanwa ta su ke kula da shagon.
“Harkar fim kuma harka ta ce da na ke kan yin ta. Harkar fim ita ce ni, ka ga kuwa in babu ita babu ni. Ko kuɗin da na buɗe shago, ai da fim na same su. Fim ba sana’ar da zan bari ba ne. Har gobe ina ci gaba da yi.”
Mawaƙin siyasa, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara), shi ne uban taro a bikin ƙaddamarwar, wato shi ne ya jagoranci buɗe shagon.
Ɗimbin ‘yan fim da su ka halarci taron sun haɗa da Adam A. Zango, Daddy Hikima, Nura M. Inuwa, Yakubu Muhammad, El-Mu’az Birniwa, Umar Gombe, Rasheeda Adamu Abdullahi, Sadiq Zazzaɓi, Hafizu Bello, Aisha Ahmad Idris (Aishatulhumaira), da Abba Miko Yakasai, Mustapha Nabraska, Siddiqa J. Sarki, da sauran su.
Rarara da Maishadda tare da su Daddy Hikima, Nura M. Inuwa da Adam Zango za su yanka zaren ƙaddamar da shagon
Ita ma matar Maishadda, tsohuwar jaruma Hassana Muhammad, ta halarci taron tare da ‘yan’uwan su na jini.
Tun wajen ƙarfe 3:00 na rana aka fara taron, amma ba a tashi ba sai wajen ƙarfe 10:00 na dare saboda cincirindon mutane.
Rarara da Daddy Hikima su na raha da Adam A. Zango

GA WANI LABARIN DAGA GWAMNATI KANO A NAN KASA:-
👇👇👇👇
Za mu samar da cibiyar koyar da sana’ar fim a Kano.
Gwamna Ganduje A Kokarin Da Yakeyi na samar da bunƙasar masana’antar finafinai ta Kannywood, gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin samar da wata cibiya domin koyar da harkar fim.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya sanar da hakan a lokacin da ya ke buɗe taron sanin makamar aiki wanda gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin gudanarwa a otal ɗin Central da ke Titin Bompai a ranar Lahadi Fimmagazine ta ruwaito.
Gwamnan ya ce, “Duba da irin muhimmancin da sana’ar fim ta ke da shi a duniya mu ka ga ya kamata mu samar maku da wasu hanyoyi na inganta sana’ar ku yadda za ta tafi da zamani da kuma ilimi. Don haka ne mu ka samar da wani tsari a yanzu na koyar da ku dabarun sanin makamar aiki da kuma ilimi a cikin harkar taku, shi ya sa mu ka taru a wannan waje domin buɗe fara koyar da ku da za a yi na tsawon kwanaki biyar saboda ku ƙara sanin yadda harkokin kasuwancin naku ya ke.”
Gwamnan ya ce hakan ya samu ne a sakamakon yadda gwamnatin sa ta damu da sana’ar fim kamar yadda su ma ‘yan fim ɗin su ke ba gwamnati goyon baya wajen gudanar da al’amurran ta.
Ya ƙara da cewa, “Duba da irin alaƙar ku da wannan gwamnati ya sa mu ka zaɓi wasu daga cikin ku mu ka saka su a cikin ƙunshin gwamnatin mu domin ku ma ku ba da taku gudunmawar a matsayin ku da ku ka daɗe ku na bayar da goyon baya a tafiyar da gwamnati.
Wasau Daga Cikin Wadanda suka halarci taron.

Ga Afakallahu nan, ɗan cikin ku ne mu ka ba shi Hukumar Tace Finafinai ya ke riƙe da ita. Kuma ga Mustapha Badamasi Nabraska shi ma S.A. ne na Farfaganda, da kuma wani babba a cikin ku da mu ka ba shi babban mai ba da shawara a kan Kannywood. Don haka mu na tare da ku kamar yadda ku ke ba mu goyon bayan ku.”
Gwamnan ya ce, “Bayan wannan hosarwa da za a yi maku, mu na da burin gina maku sabuwar cibiyar koyar da dabarun harkar fim a wannan jiha. Amma aikin zai yiwu ne idan kun haɗa kan ku kun samar da tsari a tsakanin ku, wanda hakan ne zai sa a samar da ƙwararru da za su tafiyar da harkar cibiyar.
“Don haka ina kira a gare ku da ku haɗa kan ku domin tafiya tare. Mu kuma a namu ɓangaren na gwamnati, za mu samar muku tsare-tsare masu muhimmanci a kan masana’antar ku.”
Tun da farko da ya ke nasa jawabi, shugaban Gidauniyar Kannywood, Malam Shu’aibu Yawale, ya bayyana Dakta Ganduje a matsayin gwamnan da ya bai wa masana’antar Kannywood kulawar da babu wani gwamna da ya taɓa ba ta.
Ya ce: “Babu shakka, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje shi ne gwamnan da ba a taɓa samun wani gwamna da ya ke kula da masana’antar Kannywood kamar sa ba, domin an ɗauki mutane daga cikin mu an saka su a cikin harkar gwamnati, an ɗauki nauyin karatun wasu daga cikin mu, za su tafi ƙasashen waje karatu. A yanzu kuma mu na taro ne na buɗe koyar da mu ilimin harkar fim aƙalla mutane 450
“Don haka a kullum mu ke godiya tare da jinjina ga wannan gwamnati. Kuma a shiye mu ke mu bayar da duk wata gudunmawar da ta dace don ganin gwamnati ta cimma manufofin ta da ta sa a gaba.”
Shi kuwa a nasa jawabin, malami a Jami’ar Bayero kuma masani kan harkar fim, Farfesa Abdalla Uba Adamu, kira ya yi ga ‘yan fim da su gane cewa shi fim ba kasuwanci ba ne, sana’a ne, don haka su daina tunanin samun kuɗi a lokaci guda.
Ya ce: “Duk ƙasashen da su ka ci gaba a harkar fim sun ɗauki harkar fim ne a matsayin sana’a, don haka su ke samun cigaba. Amma mu namu finafinan mun tsaya har yanzu a kan rawa da waƙa. Tun da aka faro harkar daga bidiyo aka koma sidi zuwa dibidi, har yanzu abu ɗaya ne. Babu wani abu da ake nunawa na zahirin al’adun Bahaushe ko ilimin sa da sana’o’in sa.
“Saboda haka, a yanzu da duniya ta canza aka koma YouTube, ya kamata a samu wani sauyi da za a riƙa kallon rayuwar Hausawa da cigaban da su ke da shi.”
Hadiza Mohammed, Asma’u Sani da su Teema Makamashi a taron.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa taron ya samu halartar jama’a masu yawa daga cikin masana’antar Kannywood, kuma an yi waƙoƙin siyasa tare da tallata jam’iyyar APC a wajen, wanda hakan ya sa wasu ke ƙorafin ko dai Dattawan Kannywood sun sayar da masana’antar da gwamnati ne.
An kammala taron da shirya liyafar cin abincin dare a Gidan Gwamnati, inda aka zaɓi wasu daga cikin ‘yan masana’antar aka kai su su ka ci abinci tare da gwamna.