
Yanzu Mawakan Ne Ke Jan Ragwamar Kannywood Ba Fim Ba,
An bayyana cewa yawan waƙoƙi da ‘yan fim su ke yi a yanzu su ne su ka kasance abin da masana’antar Kannywood ta ke da shi a matsayin abin yi tun bayan mutuwar kasuwancin sidi da ake bugawa a lokacin baya ana kaiwa kasuwa Folkanaija ta ruwaito.
Darakta a masana’antar, Malam Aminu S. Bono, shi ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da mujallar Fim ta yi da shi kan yanayin harkar fim a yau.
Daraktan ya ba mu ƙwarya-ƙwaryan nazarin da ya yi wa harkar fim, ya ce, “A can baya kowa ya sani kasuwar kaset ce ta riƙe masana’antar, har kuma aka dawo sidi da dibidi su ka zama su ne mu ke sayarwa. Da haka masana’antar Kannywood ta bunƙasa, aka samu arziƙi mai ɗimbin yawa a cikin harkar.
“To, daga baya kuma sai harkar sidi da dibidi ta mutu, mutane su ka karye, kowa ya riƙa ji a jikin sa.
“Ana haka, a daidai wannan lokacin sai kuma jama’a su ka yi ta shigowa cikin masana’antar duk da cewa babu fim ɗin, don haka sai kuma aka juya da yin waƙa, wadda ita kuma waƙar sai ya zama ana yin ta ne ba tare da an samar da kasuwar da za a kai ta a sayar ba. Amma dai duk da hakan sai ya zama matasa, musamman waɗanda su ka shigo harkar a lokacin da dan kuɗin su, sai su ka riƙa yin waƙoƙi, har kuma tunanin saka waƙar a ‘YouTube channels’ ya zo, kowa sai ya yi waƙa ya ɗora a ‘YouTube channel’ ko Facebook ko Instagram don kawai duniya ta san shi a matsayin jarumi, amma dai ba fim ya yi ba.
“Wannan ta sa a yanzu akwai jarumai da dama da su ka yi suna a wannan masana’antar, amma ba fim ne ya saka su ka yi suna ba, kuma kowa ya san su.”
S. Bono ya ci gaba da cewa: “Babbar matsalar da ita wannan harkar waƙar ta ke da ita shi ne ba harka ce da za ka zuba kuɗin ka kuma ka ci riba ba. Ita sai dai ka nemi suna, don haka idan ma ka zuba kuɗin ka yi waƙar, to sai dai su waɗanda su ka hau kan waƙar su yi suna, a riƙa gayyatar su wajen taro.
“Wannan ce ta sa su jaruman su ka riƙa ɗaukar nauyin waƙar su; sai su samo ‘yanmata da su ma su ka zo da son su yi fim kuma ba su samu ba, sai kawai a ƙare da waƙar.
“Hakan ya sa masana’antar Kannywood ta dogara da waƙoƙin, sai ya zama waƙar ce ta ke riƙe da masana’antar, in ban da a ɗan lokacin nan da aka fara yin finafinai masu dogon zango, amma ina tabbatar maka da cewa har yanzu waƙa ce ta ke riƙe da masana’antar Kannywood.”
Daraktan ya yi kira ga mawaƙan Kannywood da su riƙa kiyaye lafazi da kuma shigar da su ke yi a cikin waƙoƙin da su ke yi don gudun ɓata wa masana’antar Kannywood suna.
Allah Ya Taimaka.